Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Gayyaci 'Yan Wasan Da Za Su Buga Wasannin Samun Gurbin Shiga Kofin Duniya


Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)
Super Eagles (Hoto: Facebook/Super Eagles)

An bayyana sunan dan wasan kungiyar kwallon kafar kano pillars a tawagar wucin gadi ta 'yan wasa 39 wacce ta kunshi wadanda aka sani da kuma sababbi.

Super Eagles ta gayyaci tsohon dan wasan gabanta Ahmad Musa domin wasannin neman samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 wanda ya zama wajibi ne ta yi galaba a kan kasashen Rwanda da Zimbabwe, inda ya koma tawagar bayan shafe shekara guda baya nan.

An bayyana sunan dan wasan kungiyar kwallon kafar Kano Pillars a tawagar wucin gadi ta 'yan wasa 39 wacce ta kunshi wadanda aka sani da kuma sababbi.

Kociya Eric Chelle wanda tun bayan nadinsa a bara ya ke kallon gasar Najeriya, sakamakon hakan ya gayyaci wasu daga cikin taurarin gasar, abin da ke baiwa Super Eagles din da ke cikin matsananciyar bukatar farfadowa da nufin samun cancantar shiga gasar cin kofin duniyar da aka tsara kasashen Canada da Amurka da Mexico za su karbi bakunci karin dama.

Kayode Bankole na Remo Stars da Ifeanyi Onnyebuchi na Rangers da Daniel Mustapha (tsohon dan wasan Niger Tornadoes) da Ahmad Musa na daga cikin 'yan wasan dake taka leda a gida da kociyan dan asalin Mali ya gayyata.

Kamar yadda aka zata, an kuma gayyaci tawagar da ta kunshi ainihin 'yan wasan da suka kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON.

Da gwarzon dan wasan Afirka mai ci Ademola Lookman da Victor Boniface da Victor Isimhen da Ola Aina da gwarzon dan wasan baya William Troost-Ekong da Calvin Bassey da Wilfred Ndidi da kuma Alex Iwobi.

An kuma zayyana sunayen 'yan wasan da suka jima ba'a ji duriyarsu ba irinsu Joe Aribo da Cyril Dessers da Nethan Tella da Jordan Torunarigha domin fafatawar da za'a yi da kasashen Rwanda da Zimbabwe.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 0:32 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG