A yau Alhamis, motocin safa-safa dauke da fursunoni Falasdinawa suka bar kurkukun Isra’ila, bayan rudanin da aka samu yayin sakin Yahudawa 3 da ‘yan kasar Thailand 5 da ‘yan gwagwarmayar gaza suka yi ya janyo dan tsaiko a shirin.
Da goshin almuru, wani dan jaridar afp ya hangi motocin safa 2 dauke da fursunoni suna barin gidan yarin Ofer dake yammacin kogin Jordan da aka mamaye, bayan da Isra’ila tace ta samu tabbaci daga masu shiga tsakani game da sakin Yahudawa cikin aminci anan gaba.
Tunda fari a yau Alhamis da tsakar rana ofishin Firai Minista Benyamin Netanyahu, yace za’a dakatar da shirin sakin fursunoni har sai an samu tabbacin amincin da ake nema.
An tsara cewar Isra’ila za ta saki fursunoni 110, ciki har da yara kanana 30, domin musayar Yahudawa 3 da aka saki a yau Alhamis, kamar yadda wata kungiya mai fafautuka a kan Falasdinawa fursunoni ta bayyana.
Dandalin Mu Tattauna