Ministan sufurin jiragen sama da bunkasa harkokin sararin samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na kafa kamfanin kera jiragen sama a cikin kasar.
Keyamo ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da cibiyar gyare-gyare da yiwa jiragen sama garanbawul tare da tallafawa harkokin sufurinsu a Abuja.
Ya kara da cewa matakin ya dace da aniyar gwamnatin ta tallafawa kamfanonin jiragen saman Najeriya tare da bunkasa bangaren sufurin jiragen saman.
Da yake jaddada muhimmancin aikin, Ministan ya bayyana cewa shigar da karin gine-gine irinsu cibiyar bada horo, wata babbar nasara ce.
Dandalin Mu Tattauna