Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da bakin haure 113 a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja a bisa tuhume-tuhumen dake da nasaba da laifuffukan intanet, ciki har da damfara ta hanyar amfani da komfuta, tallace-tallacen damfara da halasta kudaden haram da kuma samun bayanan sirri ba bisa ka’ida ba.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ya wallafa a shafin X a yau Litinin, an gudanar da kamen ne a ranar 3 ga watan Nuwamban daya gabata, a yankin Jahi, dake wajen birnin tarayya, Abuja.
Sanarwar tace kamen ya biyo bayan samamen hadin gwiwar da cibiyar yaki da laifuffukan intanet da shiya ta 7 ta rundunar ‘yan sandan Najeriya suka gudanar.
A yayin samamen, ‘yan sanda sun kwato tarin na’urorin zamanin da aka yi ittifakin cewa dasu gungun bakin ke amfani wajen aikata laifuffukan intanet.
Kayayyakin da aka kwato sun hada komfutocin tafi da gidanka da wayoyin hannu na zamani da kananan komfutocin hannu da na’urorin samarda datar intanet ta kamfanoni da dama da injin kwakwalwar komfuta da rumbunan tara bayanan intanet da jirage marasa matuka da layukan waya da dama da na’urorin wasannin intanet da fasfo-fasfo da sauran takardun yin tafiye-tafiye.
A cikin kayayyakin da aka kwato din har da mota kirar Toyota Tundra baka da kayan kade-kade samfurin Harman/Kardon.
Dandalin Mu Tattauna