Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Almundahana: Kotu Ta Tsayar Da Ranar Sauraren Shari’ar Ganduje


Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Tuhume-tuhumen sun hada da zargin cin hanci da rashawa da wawure kudade da karkatar da dukiyar al’ummar da ta kai bilyoyin nairori.

Wata babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 20 ga watan Nuwamba mai kamawa domin sauraron dukkanin bukatun da aka gabatar mata a shari’ar zargin cin hanci da rashawa da wawure kudaden al’ummar da ake yiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane 7.

Ganduje da mai dakinsa, Hafsat Umar da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jubrilla Muhammad da wasu kamfanoni 3; Lamash Properties Limited da Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises-na fuskantar wasu tuhume-tuhume 8 da gwamnatin jihar Kano ta shigar akansu.

Tuhume-tuhumen sun hada da zargin cin hanci da rashawa da wawure kudade da karkatar da dukiyar al’ummar da ta kai bilyoyin nairori.

Shari’ar na daukar hankali saboda kimar wadanda ake karar, musamman Ganduje, wanda ya kasance shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG