Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dorinar Ruwa A Jihar Kebbi Bayan Ta Kashe Hadimin Basarake


Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri
Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri

An samu nasarar kashe dorinar ruwa da ta kashe mai gadin lambun Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi tare da raunata wani a garin Yauri a jihar Kebbi.

Gwamnan Jihar, Nasir Idris ne ya bada umurnin ga al’ummar yankin da su kashe ta.

Aliyu Gado Magatakarda Babba na sarkin Yauri yace wannan Dorinar ta kashe wani hadimin sarkin Yauri, lokacin da ya je hakon kifi. Ya kara da cewa dorinar ta jirkice kwale-kwale da yake ciki ta danne shi sai da ya mutu.

Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri
Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri

Yankin Yawuri na jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya yanki ne da ke da ruwa, inda ake hada-hadar kasuwanci da ayukkan noma da sauran wasu ayukka cikin ruwa, hakan baya rasa nasaba da yadda manyan halittun ruwa suka gidandance a yankin.

Dorina dabba ce mai hadari wadda ake samu cikin ruwa kuma garin na Yawuri ya yi suna da wannan dabbar har ma ita ce alamar tambarin garin, sai dai kwanannan an samu wata Dorina da ke da sabuwar haihuwa ta zo boyon dan da ta haifa a wani gari dake cikin ruwa a Yauri.

Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri
Dorinar ruwa da aka kashe a Yauri

Duk da yake akwai dokokin da suka tanadi a kare 'yancin dabbobi a Najeriya, a na ci gaba da fuskantar barazanar miyagun dabbobi da ke yin lahani ga bil adama a wasu sassa na kasar.

A saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

An Kashe Dorinar Ruwa A Jihar Kebbi Bayan Ta Kashe Hadimin Basarake
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG