Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Mayar Da Philip Shuaibu Kan Kujerar Mataimakin Gwamnan Edo


Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu
Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu

Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta mayar da Kwamared Philip Shaibu kan kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo watanni uku bayan tsige shi.

Mai shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ne ya yanke wannan hukuncin a zaman shari'ar yau Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotoso ya ce majalisar dokokin jihar Edo ta sabawa tanade-tanaden doka wajen sauke mataimakin gwamnan.

Alkalin ya bayyana cewa matakin tsige Shaibu ya saɓawa tsarin kundin mulkin Najeriya.

Baya ga mayar da shi, kotun ta ba da umarni a biya shi albashi da alawus alawus dinsa tun daga lokacin da aka tsige shi.

Sai dai, Majalisar Dokokin jihar Edo ta daukaka kara kan hukunci da kotun ta yanke.

Majalisar ta kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin sai kotun daukaka karar ta yanke hukunci a shari'ar.

A ranar 8 ga watan Afrilu da ya gabata ne ’yan majalisar suka tsige Kwamred Shuaibu wanda ya sha fama da takun-saka tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG