Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Malawi Ta Dakile Barkewar Cutar Kwalara


Ma'aikatan jinya a asibitin Lilongwe, Malawi, Jan. 11, 2023.
Ma'aikatan jinya a asibitin Lilongwe, Malawi, Jan. 11, 2023.

Malawi ta sanar da cewa, ta kawo karshen barkewar cutar kwalara mafi muni a kasar, cutar da ta kashe kusan mutane 2,000 tun bayan bullar ta a watan Maris din shekarar 2022.

A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya litinin, ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce, kasar ba ta samu wanda ya kamu da cutar ba ko kuma wanda ya mutu a dalinlinta cikin makonni hudun da suka gabata a cibiyoyin kiwon lafiya 26 daga cikin 29 da kasar ke da su.

Sai dai wasu masana kiwon lafiya sun ce cutar na iya sake barkewa idan kasar ta gaza magance matsalolin tsaftar muhalli da haddasa cutar.

Wata mace na dibara ruwa a Malawi
Wata mace na dibara ruwa a Malawi

Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya kaddamar da gangamin don kawo karshen barkewar cutar kwalara a watan Fabrairun bara.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce a cikin sanarwar da ta fitar ta jiya Litinin, mutane 56,376 ne suka kamu da cutar kwalara a Malawi, sannan mutane 1,772 ne suka mutu tun daga watan Maris na 2022.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG