Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Aika Matashin Da Ya Hau Hasuniyar Sabis Gwajin Kwakwalwa


Matashi da ya hau hasuniyar sabis a Abuja
Matashi da ya hau hasuniyar sabis a Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta sanar a yau, Talata 9 ga watan Yuli, 2024, cewa an aike da Shuaibu Yush'au zuwa sakatariyar cigaban jama’a (SDS) domin tantance lafiyar kwakwalwar sa.

Hakan ya biyo bayan wani mataki da ya dauka a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2024, lokacin da ya haura kan hasuniyar sabis da ke kan tsaunin babban gidan rediyon ASO da ke Katampe a Abuja, don nuna rashin amincewa da halin da ake ciki na matsin rayuwa da zargin yunkurin kashe kansa.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, Yusha'u zai fuskanci tuhume-tuhume da suka hada da yunkurin kashe kansa, da hargitsa zaman lafiyar jama’a, da kuma tunzura jama’a idan aka samu kwanciyar hankali bayan tantancewar.

Wadannan tuhume-tuhumen sun yi daidai da sashe na 231, 111, da 114 na dokar Penal Code.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda yayin da suke bayyana damuwarsu, yana mai jaddada cewa ‘yan sanda ba za su amince da kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ba.

Zanga-zangar ta Yushau ta hada da hawan tudu na hasuniyar sabis da ke kan tsauni tare da yin barazanar kashe kansa idan ba a maido da tallafin man fetur ba kuma ba a magance matsalolin rashin tsaro ba.

Wannan matakin nasa ya jawo hankalin jama’a sosai, wanda hakan ya sa jami’an tsaro da hukumonin gwamnati suka shiga tsakani, ciki har da ‘yan sanda da hukumar bada agajin gaggawa ta babban birnin tarayya Abuja, inda daga karshe suka lallashe shi ya sauka.

Da aka tsare Yushau, ya sake bayyana korafe-korafensa, inda ya bayyana matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro, da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a matsayin dalilinsa.

“Na hau kujerar naki domin wayar da kan al’amuran da suka addabi kasarmu: rashin tsaro, karancin abinci, da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta, na yi hakan ne domin in taimaka wa ‘yan Najeriya a cikin wannan kuncin da suke fama da su, kuma harma na iya bada rayuwata don ina fatan gwamnati ta dauki matakin da ya dace” inji Yusha’u.

Ya kara da cewa "idan na taimaka wa mutanen nan, ban damu da abin da ya same ni ba."

~Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG