Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NELFUND Ta Amince Da Fara Biyan Dalibai Rancen Karatu"


Taron Kungiyar WANDA Da Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 30 Wajen Fannin Abince
Taron Kungiyar WANDA Da Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai 30 Wajen Fannin Abince

Hukumar Bada Rancen Karatu ta Najeriya (NELFUND) ta amince a fara biyan rancen karatun da gwamnatin tarayya ke marawa baya ga dalibai.

Sanarwar da aka rabawa manema labarai wacce NELFUND ta wallafa a shafinta na X, na cewa an bada umarnin ne a yayin zaman daraktocin hakumar na farko daya gudana jiya Laraba a Abuja.

Sanarwar da jami’in yada labaran hukumar, Nasir Ayitogo, ya fitar tace, taron wani muhimmin mataki ne ga kudirin hukumar na baiwa dalibai tallafin kudaden karatu.

A cewar sanarwar, “a karkashin jagorancin shugaban hukumar daraktocin, Jim Ovia, babbar ajandarmu itace amincewa da sakin kudade ga daliban da suka yi nasarar samun rancen.

“Ta hanyar gaggauta sakin rancen, NELFUND ta dauki muhimmin mataki na cimma manufar data sa a gaba na tallafawa ilimi tare da bada tallafi ga shugabannin gobe.”

Hakan na zuwa ‘yan kwanaki bayan bullar rahotannin dake cewar NELFUND ta dage shirin neman rancen ga manyan makarantun jihohi saboda rashin cikakkun bayanai tsawon makonni 2.

A ranar 3 ga watan Afrilun daya gabata ne, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin rancen karatun dalibai (damar samun ilmin manyan makarantu) (wacce aka yiwa kwaskwarima) zuwa doka ta shekarar 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG