Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Bada Jimawa Ba Hadaddiyar Daular Larabawa Zata Dage Haramcin Baiwa 'Yan Najeriya Biza - Keyamo


FILE - A foreign national shows a canceled U.S. visa in his passport, having been denied entry, at Washington Dulles International Airport in Chantilly, Virginia, Feb. 6, 2017.
FILE - A foreign national shows a canceled U.S. visa in his passport, having been denied entry, at Washington Dulles International Airport in Chantilly, Virginia, Feb. 6, 2017.

Keyamo, yace an riga an cimma yarjejeniya tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan a ziyarar da tinubun ya kai kasar a watan Satumbar bara.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana shirin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, na dage haramcin bada izinin shiga kasar ga matafiyan Najeriya, nan bada jimawa ba.

Keyamo, yayin wata ganawa da babban hadimin Shugaban Kasa Bola Tinubu, Otega Ogra, wacce aka wallafa a shafin fadar shugaban kasar na YouTube a hukumance, yace an riga an cimma yarjejeniya tsakanin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa Muhammad Bin Zayed Al-Nahyan a ziyarar da tinubun ya kai kasar a watan Satumbar bara.

A cewarsa, duk da cewar Hadaddiyar Daular Larabawan ta zayyana karin ka'idojin da za'a cika kafin a dage haramcin a hukumance, tuni gwamnatin Najeriya ta kammala cikasu, abinda ya share hanyar jiran sanarwa daga gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawan.

Keyamo ya kara da cewar, "bayan ganawar shugabanin kasar, Shugaba Tinubu ya saukaka mana aiki, inda muka yi ta bibiya a matsayinmu na ministocinsa. Mun yi duk abinda ya kamata. Mu warware komai. Yanzu saura a jira sanarwar daga hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawan. Wacce tabbas tana tafe."

Keyamo ya cigaba da cewar, ya san ranar da za'a dage haramcin bada bizar, saidai ya jaddada cewar ganin damar gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawan ne ta fitar da sanarwa a hukumance.

Ana sa ran dage haramcin ya dawo da saukin yin balaguro ga 'yan Najeriya dake zuwa Dubai, kuma hakan zai inganta alaka da hadin kai tsakanin kasashen 2.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG