Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro Da Manyan Hafsoshin Tsaro Da Gwamnonin Arewacin Najeriya Sun Gana Akan Satar Mutane


Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu
Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu

Sakamakon yawaitar matsalar satar mutane a Najeriya, gwamnonin arewacin kasar sun amince da yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma duba yiyuwar yin amfani da wasu hanyoyin na daban wajen shawo kan karuwar matsalar tabarbarewar tsaro da take addabar yankin arewa.

WASHINGTON DC - An cimma wadannan shawarwari ne a yayin wani taro da mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kira tsakaninsa da kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro ciki harda Babban Sufeton 'Yan Sanda da kuma kwamandan Rundunar Tsaron Sibil Difens.

An shafe fiye da sa'o'i 4 ana gudanar da taron wanda ya gudana cikin sirri sa'annan bayan kammala shi Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe yayi karin haske game da abubuwan da aka tattauna akai.

Ya kuma bayyana shirin kungiyar gwamnonin ta yin amfani da wasu hanyoyi na daban wajen shawo kan tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya.

Gwamnan ya kara da cewar za'a nemi gudunmowar sojoji wajen murkushe masu tada kayar baya ba tare da yin amfani da karfi ba.

"Kamar yadda kuke gani, wannan taro ne tsakanin gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro da kuma mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro".

Ya cigaba da cewar, "wannan taro ne daya shafi tsaro, kuma kun san irin mahimmancin da tsaro keda shi, musammamma yanzu da matsalar yin garkuwa da mutane ke kara karuwa a shiyar arewa maso yamma, don haka akwai bukatar mu tattauna mu sake nazari tare da rungumar wasu dabarun na daban akan wadanda muke yi domin samun mafita".

A makon daya gabata ne , 'yan bindiga suka sace kusan dalibai 300 daga wata makaranta a kauyen kuriga dake karamar hukumar chikun ta jihar kaduna.

A wani taron manema labarai na daban, sojoji sun sha alwashin kubutar da ilahrin wadanda ake garkuwa dasu.

Game da satar 'yan gudun hijra a garin gamborun ngala na jihar borno kuma, sojojin sun bayyana cewar mutanen sun zartar tazarar da aka amince su je daga sansaninsu.

Haka kuma, daraktan yada labaran ma'aikatar tsaro, manjo janar edward buba, yace samun jinkiri wajen kai rahoton satar mutane na kaiwo tsaiko wajen kai daukin gaggawa daga hukumomin tsaro da sauran jama'a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG