Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
TAMBAYA 1:
“Don Allah VOA Hausa, ku tambaya min masana dan takaitaccen tarihin gidajen tarihi da kuma wuraren tarihi na Timbuktu da ke kasar Mali, wanda hukumar UNESCO ta ayyana a matsayin muhimman wuraren tarihi na duniya.
MAI TAMBAYA: Yusuf Abubakar, Bauchi, Najeriya
TAMBAYA 2:
Sai kuma kashi na biyu na amsar tambayar nan mai cewa “Salamu alaikum VOA Hausa. Don Allah ku tambaya min masana, ko me ke janyo faduwar darajar Naira a Najeriya? Shin ko me ya sa har yanzu darajar Nairar ta ke farfadowa. Shin laifin Gwamnati ne ko na yan kasuwa.”
MAI TAMBAYA: Idan an tuna, shi ne, Garba Nahali Kamba, Kebbin Najeriya.
AMSOSHI
Mun fara da amsar tambaya kan tarihin wuraren tarihi na Timbuktu da ke Mali. Masanin kayan tarihi da yadda ake adana su, da ke da zama a Abujan Najeriya, Malam Balan Karo, ya yi bayani.
Sai kuma kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambaya kan musabbabin yawan faduwar darajar Naira a Najeriya. Idan an tuna, wakilinmu a shiyyar Adamawa/Taraba a Najeriya, Muhd Salisu Lado, ya samo amsa daga Dr Ahmed Tukur Umar na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa Najeriya, wanda ya karasa bayaninsa:
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna