Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya

Zaben 2023 a Najeriya

Ku kasance da VOA Hausa kai tsaye kan zaben Najeriya na 2023 a VOAHausa.com.

Zaben 2023: Buhari Ya Koma Daura Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.

09:15 Fabrairu 27, 2023

Gwamnan Jihar Enugu Ya Fadi Zaben Majalisar Dattijai

Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya fadi zaben Majalisar dattijai a mazabar Enugu ta Arewa.

Dan takarar jam'iyar Labor Okechukwu Ezea ne ya kada gwamnan wanda ya ke cikin kungiyar gwamnonin jam'iyar PDP masu ikon fada a ji da ake kira G5.

Dan takarar jam'iyar Labor Okechukwu Ezea ya sami kuri'u 104,492, yayinda gwamnan jihar Enugu Ugwuanyi ya sami kuri'u 46,948, sai dantakar jam'iyar ANPP Ejike Eze da ya zo na uku da kuri'u 6,816.
09:21 Fabrairu 27, 2023

Tinubu Ya Lashe Zabe A Jihar Kwara

Dan takarar Jam'iyar APC, Bola Tinubu ya lashe zabe a jihar kwara.

Sanata Tinubu ya samu kuri’u 263,572 daga cikin kuri’un da aka kada, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 136,909 sai dan takarar jam’iyyar Labour , Peter Obi ya samu kuri’u 31,166.

09:26 Fabrairu 27, 2023

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ya Rasu A Lagos

Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Yagba ta Gabas a Majalisar Dokokin jihar Kogi, Jimoh Musa Omiata, ya rasu a wani asibiti da ya ke jinya a Lagos.

Omiata wanda ya fito daga al’ummar Igbagun a karamar hukumar Yagba ta Gabas ta jihar,shi ne mutum na farko da ya sake lashe zaben dan majalisar daga mazabar jihar.

Dan majalisar ya jima yana jinyar rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

11:45 Fabrairu 27, 2023

Peter Obi Ya Kada Tinubu A Legas

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar Lebour, Peter Obi ya kada babban abokin hamayyarsa a jihar Lagos, dan takarar shugaban kasa na jam'iya mai mulki Bola Tinubu a jihar Lagos.

Peter Obi ya lashe zabe a jihohi tara na jihar da ya kai ga samun nasara.

Jam'iyar Labor ta sami 582,454, APC ta sami kuri'u 572,606, yayinda jam'iyar PDP ta zo ta uku da kuri'u 75,675.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG