ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Kan Tsare Dokokin Aiki
Hukumar kula da kafafen labarai na ketare ta Amurka wato USAGM, ta hori wakilan kafafen labaru na Najeriya kan yadda za su tsare dokokin aikin jarida idan sun tashi ba da labarai kan yadda za a gudanar da babban zabe har zuwa bayan sanar da sakamako.
Zaben 2023: Kuri’arku Na Da Muhimmanci – Sakon Blinken Ga ‘Yan Najeriya
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya jaddadawa ‘yan Najeriya muhimmacin babban zaben da kasar za ta yi a karshen makon da ke tafe.
A ranar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.
“Yayin da aka tunkari zabe a Najeriya, wannan wata dama ce ga al’umar kasar da za a saurari ra’ayinsu, ta yadda za su zabawa kasar makoma mai kyau.” Blinken ya ce a wani sakon bidiyo da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.
Zaben 2023: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Iyakokin Najeriya A Ranar Asabar Da Za A Yi Zabe
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar taryya a ranar Asabar, gwamnatin tarayyar ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin kasa na kasar.
Yan Banga Sun Sace Na'urar Zabe
Shugaban Hukumar Zabe Mahmood Yakubu ya sanar da cewa, an sace na'urarorin zabe VBAS a kalla guda takwas a wadansu jihohin Najeriya 'yan sa'oi bayan bude runfunan zabe.
A jawabinsa ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, Shugaban Hukumar Zaben ya ce, an ci gaba da zaben a wadannan runfunan bayan da aka tura wadansu na'urori. Ya kuma ce an sami jinkirin fara zabe a wadansu sassan jihar Naija sakamakon hari da wadansu 'yan bindiga su ka kai.
Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma bayyana cewa, Hukumar ta fuskanci kalubale a wadansu jihohin kasar na fara zabe a makare.