Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya

Zaben 2023 a Najeriya

Ku kasance da VOA Hausa kai tsaye kan zaben Najeriya na 2023 a VOAHausa.com.

Zaben 2023: Buhari Ya Koma Daura Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.

11:50 Fabrairu 27, 2023

Atiku Ya Kada Tinubu A Yobe

Dan takarar Jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya kada Bola Tinubu dan takarar jam'iyar APC mai mulki a jihar Yobe.

Atiku Abubakar ya lashe zaben ne da kuri'u 198,567 , yayinda Bola Tinubu ya sami kuri'u 151,459.

Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar jam'yar ANPP ya zo na uku da kuri'u 18,270.

13:15 Fabrairu 27, 2023

Har Yanzu Sunan Shekaru Ke Kan Takardar Takarar ANPP A Kano

Akwai yuwuwar Hukumar Zaben Najeriya zata bayyana tsohon Gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a Majalisar dattawan kasar, muddin Jam'iyyar NNPP ta galaba a zaben da aka gudanar ranar asabar.

Hakan da ya biyo bayan rashin cire sunan sa daga kundin’yan takara na hukumar zabe ta INEC duk da cewa, ya fice daga Jam'iyyar ya koma PDP kimanin watanni uku da suka gabata.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da dakon sakamakon zaben kananan hukumomi 4 daga cikin kananan hukumomi 15 na mazabar dan majalisar dattawan ta Kano tsakiya.

Daga Mahmud Ibrahim Kwari

13:24 Fabrairu 27, 2023

Tinubu Ya Lashe Zaben Jihar Kwara

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar APC Bola Tinubu ya kashe zaben jihar Kwara.

Tinubu ya lashe zaben da kuri'u 263,572, Atiku Abubakar na jam'iyar PDP ya samu kuri'u 136,909, yayinda Peter Obi, ya sami kuri'u 31,166,Rabiu Kwankwaso, ya sami kuri'u 3,141.

13:31 Fabrairu 27, 2023

Atiku Ya Lashe Zaben Jihar Osun

Dan Takarar Jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben jihar Osun.

Atiku ya lashe zaben ne da kuri'u 354,366, yayinda abokin hamayyarsa na kurkusa a jihar Bola Tinubu na jam'iyar APC ya sami kuri'u 343,945, sai Peter Obi, da ya samu kuri'u 23,283, yayinda Rabiu Kwankwaso, ya sami kuri'u 713.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG