Atiku Ya Lashe Zabe A Jihar Katsina
Dan takarar shugaban kasa na babbar Jam'iar adawa PDP, Atiku Abubakar, ya kada dan takarar jam'iya mai mulki Bola Tinubu a jihar Katsina, jihar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Atiku Abubakar ya lashe zabe da kuri'u 489,045, yayinda Bola Tinubu ya sami kuri'u 482,283.
Dan takarar jam'iyar ANPP Rabi'u Kwankwaso ya zo na uku da kuri'u 69,386.
Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawal Ya Lashe Zabe
Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawal ya lashe zabe domin wakilcin Yobe ta Arewa, da zai bashi damar komawar Majalisa, duk da kayen da ya sha a mazabarsa.
Ahmed Lawal ya lashe zabe da kuri'u 91,318, ya doke abokin hamayyarsa na jam'iyar PDP Bello Ilu da ya zo na biyu wanda ya sami kuri'u 22,849.
Tinubu Ya Lashe Zabe A Jihohin Ondo da Ogun
Dan takarar jam'iyar APC Bola Tinubu ya lashe zabe a jihohin Ondo da Ogun.
Bola Tinubu ya lashe zabe a jihar Ogun da kuri'u 341,554, Atiku Abukar ya sami kuri'u 123,831, yayinda Peter Obi ya zo na uku da kuri'u 85,829, sai kuma Rabi'u Kwankwaso mai kuri'u 2,200.
A jihar Ondo, Bola Tinubu ya sami kuri'u 369,924, Atiku ya sami kuri'u 115,463 , Peter Obi ya sami kuri'u 47,350, yayinda Rabi'u Kwankwaso ya sami kuri'u 930 .
Jam'iyar SDP Ta Kada APC A Mazabar Shugaban Jam'iya Mai Mulki
Jam'iyar APC ta sha kaye a mazabar shugaban jam'iyar na kasa Abdullahi Adamu, ta rasa kujerar Majalisar Dattijai ta shugaban jam'iyar.
Dan takarrar jam'iyar SDP Ahmed Wadada ya doke babban abokin hamayyarsa na jam'iyar APC, Shehu Tukur a shiyyar Nasarawa ta Yamma.
Ahmed Wada ya samu kuri’u 96,488, yayin da APC ta samu kuri’u 47,717, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 46,820, sai kuma jam’iyyar Labour. (LP) 33,228.