Ba Za A Ci Gaba Da Gudanar Da Zabe A Jihar Plato Ba-INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jahar Filato tace ba za'a ci gaba da gudanar da zaɓe a rumfunan zabe da basu kammala zaben a jiya asabar ba.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa daga Fasto Yusuf Jakheng daga rumfar zabe na 085 a harabar Cocin dake "Narguta B" a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Jakheng yace jami'an hukumar INEC sun zo rumfar zaben da safiyar yau Lahadi inda suka shaida wa masu zaben cewa saboda yadda aka tsara naurar tantance masu jefa kuri'a BVAS, duk wani canje-canjen da za a yi don bude shi, zai share dukan bayanan da ke ciki.
Sanarwar tace an tsara naurar BVAS ne ta daina aiki da kanta daga karfe goma na daren ranar asabar 25/02/2023.
Daga Zainab Babaji, Jos, Nigeria
Direbobin Motocin Haya Sun Kawo Saiko A Tattara Sakamakon Zabe A Jihar Enugu
Har yanzu ana ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisar Najeriya a jihohin kudu maso gabas, yayin da ake ci gaba da yin zabe yau a wasu rumfunan zabe a wasu jihohin yankin kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta tsara.
Ko da yake har yanzu ba a gano ainihin abin da ke jinkirta isowar akasarin sakamakon zabe daga kananan hukumomin zuwa shelkwatar hukumar zabe a babban biranen jihohin yankin ba, kakakin hukumar zabe ta kasa a jihar Inugu Mista Amuchia Chuks na ganin jinkirin ba zai rasa nasaba da matsalar da hukumar INEC ta fara fuskanta tun jiya Asabar a hannun kungiyoyin sufurin da aka basu kwangilar jigilar kayayyakin zabe ba.
Mista Amuchia Chuks ya shaida wa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, hukumar zabe ta kasa INEC ta shiga yarjejeniyar jigilar kayayyakin zabe da kungiyoyin NURTW da NARTO inda aka aminta da biyansu kashi hamsin cikin dari na kudinsu don isar da kayayyakin zabe sassa daban-daban na kasar, kana a biya su raguwar kudin idan suka kammala aikinsu. Sai dai an sami sabani da wadansu direbobin da suka ki zuwa wadansu wuraren da aka tura su kai kayan aiki.
Daga Alphonsus Okoroigwe, Enugu
An Fara Sanar Da Sakamakon Zabe A Jihar Kano
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a jihar Kan ta fara sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa na Majalisun Tarayya da aka gudanar jiya.
Farfesa Lawal Suleman Bilbis na Jami’ar Usman Dan Fodio a Sokoto shi ne ke karban sakamakon zaben daga turawan zabe.
I zuwa yanzu an sami sakamakon zaben kananan hukumomi 9 daga cikin 44. Ana kyautata zaton kammala tattara sakamakon zaben jihar tsakanin daren yau zuwa safiyar gobe.
Daga Baraka Bashir
Tinubu Ya Lashe Zabe A Dukan Kananan Hukumomin Jihar Ekiti
Dan takarar jam'iyar APC Bola Tinubu ya lashe zabe a dukan kananan hukumomin jihar Ekiti goma sha shidda.
Bisa ga sakamakon zaben da babban jami'i mai sanar da sakamakon a jihar Farfessa Akeem ya sanar, Tinubu ya sami kuri'u 201,494, ya doke abokin hamayyar da ke biye da shi kurkusa Atiku Abukar dan takarar jam'iyar PDP wanda ya sami kuri'u 89,554