Za A Fara Sanar Da Sakamakon Zabe Yau Da Yamma
Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar a cewa, za’a fara sanar da sakamakon zabe daga karfe shida na yamma agogon Najeriya
A rana ta biyu da fara zaben Shugaban kasa da na Majalisun tarayya, Hukumar Zaben Najeriya tace zata fara karba tare da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa daga baturan zabe, da misalin karfe shida na 'yammacin Lahadi agogon Najeriya.
INEC Ta Bude Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Abuja
- By Mahmud Lalo
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta sanar da bude cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a hukumance a ranar Lahadi a Abuja.
A ranar Asabar aka gudanar da zaben, ko da yake, wasu yankuna a sassan kasar na ci gaba da kada a kuri’a.
“Ina mai sanar da bude wannan cibiya a hukumance wacce za ta fara aiki har zuwa lokacin da za a sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.” Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce.
Farfesa Yakubu ya kara da cewa, cibiyar za ta ci gaba da kasance a bude ba dare ba rana, amma za a rika zuwa dan takaitaccen hutu.
Mazauna Birnin Abuja Sun Bayyana Gamsuwa Da Tsarin Zaben Bana
Wadansu mazauna unguwanni da ke yankunan kananan hukumomin Bwari, Gwagwalada da wasu sassan birnin tarayya Abuja, sun bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na Majalisun tarayya duk da matsalolin da aka fuskata a wadansu wurare.
A hirar su da Muryar Amurka yayin da su ke dakon sakamakon zaben, sun bayyana cewa, amfani da nau’rar tantance mai kada kuri’a da Hukumar Zabe ta yi, ya ba mutane kwarin guiwa cewa, wannan karon za a kimanta gaskiya.
Zaben ya fi jan hankali a birnin Abuja, musamman fafatawar da aka yi tsanakin Dan Majalisa mai ci Philip Tanimu Aduda na jam’iyyar PDP da kuma Alhaji zakari Angulu Dobi na jam’iyyar APC, wadanda dukkanninsu tsoffin ‘yan Majalisar Wakilai ta Tarayya ne, dake da gogewa a siyasar babban birnin Tarayya, da kuma suke da magoya baya daidai gwargwado.
Hassan Maina Kaina, daga Abuja
Buhari Ya Jajintawa ‘Yan kasuwar Da Ibtila’in Gobara Ya Shafa A Jihar Borno
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar dauke da sa hannun kakakin Shugaba Buhari Malam Garba Shehu a ranar Lahadi, ta ce gobarar, babban ala’mari ne da ya tba zukatan ‘yan Najeriya.
“Shugaban Najeriya yana kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan duba da cewa yanzu ana yanayi ne na da iska ke kadawa, wacce ke saurin haddasa tashin gobara a dazuka, gidaje da sauran gine-gine.” Sanarwar ta ce.
Buhari ya kuma yaba da irin matakan gaggawa na tallafi da gwamnatin jihar ta dauka, yana mai kira da a samar da hadin kai tsakanin ma'aikatun jihar ta Borno da na tarayya wajen samawa wadanda abin ya shafa sa’ida.