An Kama Wani Jami'in Hukumar Zabe Bisa Zargin Karbar Na Goro
An kama wani jami'i Hukumar Zabe a mazabar mandari bisa zargin aikata zamba cikin aminci inda ake zargin shi da karbar wadansu kudade da nufin ba wata jam'iyar galaba.
Bayanai na nuni da cewa, tuni aka mika jami'in da aka saya sunansa ga hukuma.
A halin da ake ciki kuma. binciken da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa an kammala zabuka a kwaryar Kano tare kuma da kammala tattara sakamakon zabe a mafiya yawan mazabun da Muryar Amurka ta ziyarta.
Tuni jami'an zabe suka fara hallarta ofishin Hukumar Zabe n ajiha inda Jim’in Hulda da jama’a Mai Maulud ya ce da misalin karfe 2 na rana za’a fara karbar sakamakon mazabun da ke jihar.
Baraka Bashir, daga Kano.
Ana Kan Tattara Sakamakon Zabe A Jihar Kaduna
Bayanai daga jihar Kaduna na nuni da cewa, har yanzu babu karamar hukumar da ta kammala tattara sakamakon zabe a fadin jahar Kaduna.
Duk da shirin karban sakamakon zabe daga kananan hukumomin jahar , Hukumar zabe a jahar Kaduna ta ce har yanzu jami'an zabe a kananan hukumomi 23 na jahar, ba su kammala tattara sakamakon maza bu ba.
Binciken da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa, an fara zabe a makare a wurare da dama sakamakon rashi isar jami'an gudanar da zabe da wuri da kuma tangarda da aka rika samu da na'urar tantance mai zabe.
Isa Lawal Ikara, daga Kaduna
An Kaddamar Da Aikin Tattara Sakamakon Zabe
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya kaddamar da aikin tattara sakamakon zaben Shugaban kasa na na 'yan Majalisun Tarrayya da aka gudanar jiya Asabar.
A jawabinsa yayin kaddamar da shirin, Shugaban Hukumar Zaben ya karanta ka'idojin tattarawa da sanar da sakamakon zabe da za a yi a babban zauren taron kasa da kasa da ke babban birnin Tarayya Abuja.
Za a sanar da sakamakon zaben ne a gaban kungiyoyin sa ido da suka fito daga kasashe da cibiyoyin cikin gida da kuma sauran kasashen duniya, da kuma daruruwan kafofin watsa labarai.
Ana Kan Gudanar Da Zabe A Jihar Ribas
Yanzu haka ana can ana gudanar da zabuka a mazabu 141 na jihar Bayelsa kwana guda bayan kammala zaben Shugaban kasa da na 'Yan Majalisun Tarayyar Najeriya a duk fadin kasar.
Wannan ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula da suka tilasta sake gudanar da zabuka a wasu sassan jihar.
Rahotanni daga jihar Delta kuma na nuni da cewa, dan sanda daya ya rasa ransa yayin tashin hankali a wajen zabe.
Lamido Abubakar, daga Fatakwal