Abinda Ya Sa Na Nuna Katin Zabe Na-Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya nuna katin zabensa kafin jefa shi akwati a mazabarsa da ke Daura inda ya kada kuri'a.
A hirar shi da manema labarin jim kadan bayan ya kada kuri'a, Shugaba Buhari ya ce ya nuna katin kuri'ar shi ne a fili bayan ya dangwala hannu, domin ya tabbatar wa kowa cewa, ya zabi dan takarar jam'iyarshi ta APC , Bola Tinubu.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, bayyana kuri'ar da ya yi manuniya ce cewa, yana tare da am'iyarshi.
Ana Shirin Fara Sanar Da Sakamakon Zabe A Abuja
Yau ake kyautata zaton za a fara sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa da na Majalisun Tarayyar Najeriya da aka gudanar jiya.
Duk da yake ba a kammala gudanar da zabe a wadansu mazabun jihohin kasar ba, shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa, za a fara sanar da sakamakon zabe yau da karfe 12 na rana.
Nan da kasa da mintoci 20 Shugaban Hukumar Zabe zai yi wa manema labarai jawabi dangane da zaben.
Yanzu haka dai, kafofin watsa labarin na ta shirye shiryen watsa sakamakon zaben a babban zaure taro na kasa da kasa da ke birnin Tarayya Abuja da ke karkashin cikakken tsaro.
An Yi Gobara A Wata Kasuwa Da Ke Maiduguri
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na nuni da cewa, gobara ta tashi a wata kasuwa da ake kira "Monday Market" da safiyar yau Lahadi, a daidai lokacin da ake tattara sakamakon zaben Shugaban kasa da na 'yan Majalisun Tarayya da aka gudanar jiya.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, wutar ta tashi ne a wadansu shaguna da misalin karfe daya na asuba. Bisa ga rahoton, da misalin karfe goma da rabi, wadansu zauna gari banza da suka fusakata sakamakon rashin kai dauki cikin gaggawa, sun shiga lalata kaddarorin jama'a kafin hukumomi su shawo kan lamarin.
Babu tabbacin masababin tashin gobarar.
An Dage Lokacin Bude Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC , ta tura lokacin bude cibiyar tattara sakamakon zabe daga karfe 12 na rana zuwa karfe daya.
Da farko an sanar da cewa, Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Mahmood Yakubu zai kaddamar da aikin tattara sakamakon zabe da karfe 12 ranar yau, lokacin da aka zaci za a fara sanar da sakamakon zaben.
A wata hira da Muryar Amurka, kwamishinan watsa labarai na hukumar Festus Okoye ya bayyana cewa, i zuwa yanzu, ba a tura wa hukumar sakamakon zaben ko jiha daya ba. Ya kuma bayyana cewa, yana yiwuwa a fara sanar da sakamakon zaben a daren yau Lahadi idan an samu da wuri, idan ba haka ba kuma a fara sanar da sakamakon zaben gobe da safe.