Har Yanzu Ana Kada Kuri'a A Wasu Rumfunan Zabe
- By Murtala Sanyinna
Yayin da tuni da wasu rumfunan zabe suka nade tabarmar jefa kuri'a, har ya zuwa karfe 6 na yamma (agogon Najeriya) ba'a kammala zabe ba a wasu mazabu saboda wasu dalilai da dama.
A wasu rumfunan zabe, kamar a mazabar Getsi da ke Tudun Murtala, a cikin karamar hukumar mulkin Nassarawa ta jihar Kano, an sami tsaiko sosai wajen isar kayayyakin zabe. Wakiliyar Sashen Hausa ta ce an soma tantance masu zabe a mazabar ne da misalin karfe 2 na rana, kuma har kawo yanzu ana ci gaba da zabe a mazabar.
Wasu mazabu kuwa kamar yadda muke samun rahoto, jami'ai da kayayyakin zaben sun isa cikin lokaci, to amma yawan masu zabe da suka yi turuwa ya sa har kawo yanzu ba'a kammala jefa kuri'a ba. A wasu rumfunan kuma cinkoson jama'a din ya haifar da 'yar hatsaniya, wadda kuma ta dan kawo tsaiko wajen gudanar da zaben.
INEC Ta Tsawaita Zabe Zuwa Lahadi Wasu Rumfunan Zaben Jihar Bayelsa
- By Murtala Sanyinna
Hukuma zaben Najeriya ta INEC ta ce an dage gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya na ranar Assabar zuwa Lahadi a wasu mazabun jihar Bayelsa.
Hakan ko ya biyo ne bayan hatsaniya da ta barke a yayin soma gudanar da zabe a mazabu 4 da suka kumshi rumfuna zabe 141 a Yenagua babban birnin jihar, lamarin da ya sa tilas aka jingine kada kuri'a.
Yayin da ya ke zantawa da manema labarai a babbar cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja da yammacin ranar Assabar, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ya zuwa lokacin, jami'an tsaro sun sami shawo kan rikicin.
To sai dai kuma ya ce a yayin da ake shirin ci gaba da soma zaben, jami'an zabe wadanda akasarinsu 'yan hidimar kasa ne na NYSC, sun bayyana fargabar ci gaba da aikin a cikin yanayin.
Za A Gudanar Da Zabe A Wadansu Mazabun Birnin Jos Yau Lahadi
Rumfunan zabe da dama ne zasu ci gaba da gudanar da zabe a yau lahadi a cikin birnin Jos.
Duk da shike Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa a jahar Filato ba ta fito da sanarwa ko amsa kira ko sako da na aike wa jami'inta Malam Shehu Baba ba, rumfunan zabe da dama a yankin "Narguta B" dake karamar hukumar Jos ta Arewa basu kammala zabe a jiya asabar ba.
Wadansu mutane da Muryar Amurka ta zanta da su kan matsalolin da suka kawo tarnaki a zaben sun bayyana rashin zuwan jami'an zabe da kayan aiki a kan lokaci, da matsalar na'urar tantance masu kada kuri'a, BVAS, Wanda kan yi zafi ya daina aiki.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ayyana ci gaba da gudanar da zaben a wadansu jihohi goma sha biyar da birnin tarayya Abuja, sai dai bai sanya jahar Filato a cikin jihohin da za'a ci gaba da zaben a yau Lahadi ba.
Zainab Babaji, daga Jos.
An Fara Samun Sakamakon Zabe A Wadansu Mazabun Jihar Legas
Bayan kammala zaben shugaban kasa da na Majalisun kasa a Najeriya, yanzu hankali ya karkata zuwa sanin sakamakon zabe daga Hukumar zabe ta kasa.
A birnin Legas yanzu haka an fara samun sakamakon zabe daga mazabu daban daban na jihar.
Rahotannin da muryar Amurka ta samu na cewa, an samu tashin hankali a wasu wurare inda matasa suka yi anfani da bindiga wajen tarwatsa masu zabe.
Sai dai hukumar zabe tace wannan ba zai kawo cikas ga sakamakon zaben jihar ba.
Rahotanni na nuna cewa an gudanar da zaben cikin kwanciuar hankali.
Yanzu haka dai hedekwatar hukumar zaben reshen jihar Legas ta fara daukan harami.
Babangida Jibril, daga legas