ZABEN 2023: Masu Larura Ta Musamman Sun Koka
- By Murtala Sanyinna
Duk da yake hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi ta jaddada cewa ta yi tanadi na musammam domin baiwa masu dauke da larura ta musamman damar shiga dumu-dumu a babban zaben kasar na 2023, wasu masu larura sun yi korafin karancin tanadin da aka yi musu alkawari.
Hukumar zaben ta ce za ta samar da wasu na'urori da kayayyakin taimakawa masu nakasa, kamar na kara ji da gani a rumfunan zabe a zaben na bana.
To sai dai kuma wasu masu fama da larura ta musamman da wakilinmu ya zanta da su a jihar Sokoto, sun ce ba bu isassun na'urorin a mafi yawan rumfunan zabe.
'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Kada Kuri'a A Mazabunsu
'Yan takarar shugaban kasa na dukan jam'iyun kasar sun kada kuri'a a mazabunsu inda dukansu su ka yi kirarin cewa, za su yi nasara.
Da yake kada kuria' a mazabarshi da ke Ward 2, a Kauyen Amatoto, karamar hukumar Anaochi, dan takar jam'iyar Labor Peter Obi ya shaidawa manema labarai cewa, idan akwai dan takarar da ya kamata sauran 'yan takara su sauka su bar mashi, to shine, sabili da shi ne yake da kuzarin shugabanci.
A hirar shi da manema labarai bayan kada kuri'a a mazabarshi da ke Aliya 02, da ke Gwadabawa a Karamar Hukumar Yola ta Arewa, dan takarar jam'iyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana gaba gadin samun nasara.
Shi ma a nashi bayanin, bayan kada kuri'a a mazabar Kwankwaso Malamai, Tandu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyar ANPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce yana da kwarin guiwa cewa, zai yi nasara.
Dan takarar jam'iyar APC Bola Ahmed Tinubu wanda ya kada kuri'a a mazabar 085, 3, Alausa, Ikeja, ya ce jam'iyar tana da gagarumin goyon baya da kuma kwarin guiwar samun nasara.
An Rufe Wasu Rumfunan Zabe
- By Murtala Sanyinna
Yanzu haka an kammala kada kuri'a a akasarin rumfunan zabe, kuma tuni aka soma lissafa kuri'u a matakin mazabu, na zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki na tarayya.
Peter Obi Ya Gamsu Da Tsarin Zabe
- By Murtala Sanyinna
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya ce ya gamsu da yadda zaben shugaban kasa ya gudana.
Obi ya ce bai ga wata babbar matsala ba a inda ya jefa kuri’a, haka kuma a rahotannin da yake samu, ba inda ya ji wata mummunar matsala da kan iya kawo cikas ga zaben.
Sai dai ya jaddada cewa yana nan tsaye kaimun daga farko har ya zuwa karshen zabe a matsayin dan takarar shugaban kasa, wato ba zai janye wa kowa ba ke nan.