Najeriya: Wasu Jam'iyyun Adawa Sun Nemi A Soke Zaben Shugaban Kasa
Jami’yyun adawa na PDP, LP da ADC, sun yi kira da a soke zaben shugaban kasar da aka yi, suna masu cewa an tafka magudi a zaben.
Shugabannin jam’iyyun sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a Abuja a ranar Talata.
Sai dai hukumar zabe ta INEC, ta ce zargin na su ba shi da tushe balle makama.
INEC Ta Ayyana Obi A Matsayin Wanda Ya Fi Yawan Kuri'u A Jihar Imo
Hukumar zabe ta INEC, ta ayyana dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi, a matsayin wanda ya fi yawan kuri’u a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Obi (LP) – 352, 904
Tinubu (APC) – 66,171
Atiku (PDP) – 30, 004
Kwankwaso (NNPP) – 1,536
Hukumar Zabe Ta Sake Tura Lokacin Sanar Da Sakamakon Zabe
Hukumar zabe ta sake tura lokacin ci gaba da sanar da sakamakon zabe, a rana ta uku da fara sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar.
A bayaninsa, tsohon darektan wayar da kan jama'a kan harkokin zabe, Barrista Osazi Uzi, ya bayyana cewa, yanzu haka tuwaran zabe sun riga sun iso da sakamakon zaben jihohi bakwai, kuma hudu sun riga sun iso tashar jirgin sama ta birnin Tarayya Abuja, yayinda wadansu kuma ke kan hanya, sabili da haka Hukumar ta tsaida shawarar sake tura lokacin ci gaba da sanar da sakamakon zaben zuwa karfe uku da rabi na yamma.
Matasa Sun Fara Gangami Kan Sakamakon Zabe
Wadansu matasa sun fara gangami a titunan babban birnin tarayya Abuja.
Matasan sun yi dafifi a mahadun manyan hanyoyi suna rike da kwalaye dauke da rubutu da ke cewa, "Mu mamaye hukumar zabe yanzu, Tilas ne kuri'a ta, ta yi tasiri, Najeriya ba ta sayarwa ba ce, Muna neman adalci, A dawo da na'urar tattara sakamakon zabe IREV, Ba IREV ba karbar sakamakon zabe." da dai sauransu.