Hukumar Zabe Ta Daga Lokacin Sanar Da Sakamako
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta tura lokacin fara sanar da sakamakon zabe daga karfe sha daya na safe zuwa karfe biyu na rana.
Hukumar ta sanar da cewa, yanzu haka tana jiran sakamakon zaben jihohi hudu da ke kan hanyar zuwa Abuja, ta kuma bayyana cewa, da zarar sun iso, za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben har zuwa lokacin da za a kammala dukan wadanda ke hannu.
Atiku Ya Samu Nasara a Sokoto
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Babban jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Kabiru Bala, wanda shi ne shugaban jami’ar ABU Zaria ne ya gabatar da sakamakon a ranar Talata.
Atiku ya samu kuri’a 288,679 yayin da Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 285,444.
Peter Obi na Labour Party ya samu kuri’a 6,568 yayin da Rabiu Kwankwaso na NNPP ya samu kuri’a 1,300.
Peter Obi Ya Lashe Abuja
- By Mahmud Lalo
Dan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya lashe zaben shugaban kasa a Abuja, babban birnin Najeriya da gagarumar nasara.
Obi ya samu nasarar lashe kananan hukumomi hudu daga cikin shida da ke birnin, wadanda suka hada da Bwari, Kuje, Gwagwalada da AMAC.
Hukumar zabe ta INEC ta sanar cewa Obi ya samu kuri’a 281,717 yayin da APC ta samu kuri’a 90,912. Jam’iyyar PDP kuwa ta samu kuri’a 74,193 a zaben kamar yadda INEC ta sanar.
Shekarau Ya Sake Lashe Kujerar Sanata A Mazabar Kano ta Tsakiya
- By Mahmud Lalo
Hukumar zabe ta INEC a jihar Kano ta ayyana tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata a mazabar Kano ta Tsakiya.
Babban jami’in zabe a jihar, Farfsesa Tijjani Hassan Darma ne ya bayyana nasarar Shekarau wanda zai je majalisar dattawan a karo na biyu.
Shekarau wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP ya koma jam’iyyar PDP gabanin zaben, ya samu kuri’a 456, 787 yayin da babban abooin hamayyarsa na APC, Alhaji Abdulkarim Zaura ya samu kuri’a 168,677, kamar yadda INEC ta sanar.