Obasanjo Ya Yi Kira Da A Soke Sakamakon Zabukan Wadansu Mazabu
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi kira da a soke sakamakon zabe a yankunan da aka karkata akalar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato BVAS da sabar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Obasanjo ya bukaci hakan ne a wata wasika da ya rubuta yau Litinin inda ya ja kunnen shugaban kasa Muhammadu Buhari kan magudin sakamakon zabe.
Ya yi kira ga Buhari da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Mahmood Yakubu da su guji abin da ya bayyana a matsayin hadari da kuma bala’i da ke jiran faruwa.
Peter Obi Ya Lashe Zabe A Jihar Nassarawa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour , Peter Obi, ya lashe zabe a jihar Nassarawa.
Peter Obi ya lashe zaben da kuri'u 191,361 inda ya doke sauran 'yan takara a zaben.
Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 172,922 ya zo na biyu, yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri’u 147,093 ya zo na uku a karshen zaben jihar. Yayinda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Musa Kwankwaso, ya zo na hudu da kuri'u 12,715.
Wakilan Jam'iyun Siyasa Sun Bukaci Sakel A Sanar Da Sakamakon Zabe
Wakilan manyan jam'iyun hammaya da su ka shiga takarar shugaban kasa sun bukaci Hukumar Zabe ta dakatar da sanar da sakamakon zabe sai an tabbatar da sahihancin sakamakon da Baturan zabe ke gabatarwa.
Wakilan jam'iyun sun bayyana rashin gamsuwa da sakamakon zaben da ake sanarwa a babban zauren taron kasa da kasa da ke birnin tarayya Abuja, da su ka ce ya sabawa alkawarin da Hukumar Zabe ta yi na yin amfani da na'ura wajen tattarawa da yayata sakamakon zaben kai tsaye ga 'yan Najeriya.
Bakin wakilan ya zo daya a kan wannan matsayar banda ta wakilan jam'iyar APC da YPP da kuma na NRM wadanda su ka ce a ci gaba da sanar da sakamakon zaben ba lallai sai an bi tsarin da Hukumar Zabe ta yi alkawarin amfani da shi na sanar da sakamakon zaben ba.
Atiku Ya Lashe Zaben Jihar Adamawa
Dan takarar na PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben a jihar shi Adamawa a gagarumin rinjaye.
Atiku ya samu kuri'u 417,611 yayin da dan takarar jam'iyar APC Bola Tinubu da ke biye da shi a matsayi na biyu ya samu kuri'u 182,881, sai Peter da Obi na jam'iyar Labour kuri'u 105,645, yayinda Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya zo na hudu da kuri'u 8,006.