Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya

Zaben 2023 a Najeriya

Ku kasance da VOA Hausa kai tsaye kan zaben Najeriya na 2023 a VOAHausa.com.

Zaben 2023: Buhari Ya Koma Daura Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.

15:14 Fabrairu 27, 2023

Yan Hamaiya Sun Yi Watsi Da Tsarin Gabatar Da Sakamon Zaben Najeriya

Wakilan jam'iyyun hamaiya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.

Dakin gabatar da sakamakon zabe na kasa da ke Abuja ya kusa hargitsewa da muhawara a lokacin da a ka bayyana sakamakon jihohin Kwara da Osun da kuma Ondo.

Wakilin jam'iyyar PDP, Dino Melaye, shine akan gaba a nuna sam ba a bin ka'ida wajen baiyana sakamakon don ba a gabatar da ainihin sakamakon da a ka dauko daga jihohi.

15:03 Fabrairu 27, 2023

Mijin Jarumar Fina-Finai Mercy Johnson Ya Lashe Zaben Majalisar Wakilai

Mijin fitacciyar jarumar nan mai suna Mercy Johnson ya lashe zaben kujerar Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Esan Kudu maso Gabas/ Esan -Gabas, a jihar Edo a zaben da aka gudanar ranar asabar.

Prince Odianosen Okojie, wanda ya tsaya takara karkashin jam’iyyar APC, ya samu kuri’u 21,764. ya doke dan takarar jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 10,007 da kuma dan takarar jam’iyyar Labour wanda ya samu 11,528.

14:55 Fabrairu 27, 2023

Tinubu Ya Lashe Zabe A Jihar Jigawa

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar APC Bola Tinubu ya lashe zabe a jihar Jigawa.

Bola Tinubu ya sami kuri'u 421,390, yayinda Jam'iyar PDP ta sami kuri'u 386,587, NNPP 98,234 sai kuma jam'iyar Labour da ta sami kuri'u 1,889.

14:51 Fabrairu 27, 2023

Wakilan Jam'iyun Hamayya Sun Yi Watsi Da Sakamakon Zabe

Wakilan jam'iyyun hamayya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.

Wakilin jam'iyyar PDP Dino Melaye da ke kan gaba ya nuna rashin amincewa da yadda aka yi watsi da ka'idar fitar da sakamakon zabe, ya kuma nuna ba zasu yadda a ci gaba da gabatar da sakamakon zaben ba sai baturan zabe sun rantse cewa, abinda su ke gabatarwa daidai yake da sakamakon da na'ura ta dauka.

Kazalia Melaye ya ce ya zama wajibi a rika nuna sakamako da na'urar BVAS mai hana magudi ta dauka tare da sakamakon takarda. Shi ma wakilin jam'iyyar Leba Umar Ibrahim ya ce ba za su yarda da tsarin gabatar da sakamakon ba.

Daga Nasiru Adami El-Hikaya

Domin Kari

XS
SM
MD
LG