Karancin Fitowar Masu Zabe A Kaduna
- By Murtala Sanyinna
A jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya an sami karancin fitowar masu kada kuri'a a rumfunan zabe, sabanin yadda lamarin ya kasance a zabukan baya.
Haka kuma akwai rahotannin da ke cewa an sami makara wajen isar da kayayyakin aiki a rumfunan zabe, Lamarin da ya sa gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi jira na tsawon fiye da sa'a daya a rumfar zabe kafin ya sami damar kada kuria.
Kasuwar Wasu Ta Bude A Runfunan Zabe
Masu zabe a sassa daban-daban na Abuja sun nuna gamsuwa kan aikin na’urar tantance masu kada kuri’a wato BVAS da hukumar zabe ke amfani da ita a babban zaben da bugin kirjin hanya ce ta magance magudin zabe.
A rumfuna da dama da mu ka zagaya mun ga masu zabe su na kan layi su na kada kuria’r su ba tare da samun cikas ba. Wakilan jam’iyyu na sanya ido kan zaben da nuna kyakkyawar fata cewa za a kammala zaben lafiya kuma gwanayen su za su samu nasara.
Wani abun da ya dauki hankali shi ne sabbin rumfunan zabe da a ka kirkiro inda a wata rumfa a anguwar AREA 3 a Abuja a ke da masu zabe 6 kacal alhali akwai jami’ai kusan 7 da ke kula da rumfar.
Jami'an Zabe Sun Fi Masu Kada Kuri'a Yawa A Wata Mazabar Abuja

An Fuskanci Lalacewar Na'urorin VBAS A Wasu Sassan Jihar PLato
Rahotanni daga wasu rumfunan zabe a Jos, jihar Filato sun nuna cewa wasu na'urar tantance masu jefa kuri'a, BVAS sun samu matsala, kayan zabe sun isa a makare, a wasu wuraren da karfe 11:40 na safe jami’an zabe ba su isa wasu rumfunan zabe a tsakiyar birnin ba.
Ko da yake hukumar zabe INEC ta gyara wasu, amma ba su canza ba har zuwa lokacin da ake aike wannan rahoto.
An kuma fara kada kuri'a da karfe 8:30 na safe a wasu rumfunan zabe a fadin jihar. Zainab Babaji.