Yan Banga Sun Sace Na'urar Zabe
Shugaban Hukumar Zabe Mahmood Yakubu ya sanar da cewa, an sace na'urarorin zabe VBAS a kalla guda takwas a wadansu jihohin Najeriya 'yan sa'oi bayan bude runfunan zabe.
A jawabinsa ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, Shugaban Hukumar Zaben ya ce, an ci gaba da zaben a wadannan runfunan bayan da aka tura wadansu na'urori. Ya kuma ce an sami jinkirin fara zabe a wadansu sassan jihar Naija sakamakon hari da wadansu 'yan bindiga su ka kai.
Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma bayyana cewa, Hukumar ta fuskanci kalubale a wadansu jihohin kasar na fara zabe a makare.
Zaben 2023: Gwamnati Ta Bada Umarnin Rufe Iyakokin Najeriya A Ranar Asabar Da Za A Yi Zabe
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar taryya a ranar Asabar, gwamnatin tarayyar ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin kasa na kasar.
Zaben 2023: Kuri’arku Na Da Muhimmanci – Sakon Blinken Ga ‘Yan Najeriya
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya jaddadawa ‘yan Najeriya muhimmacin babban zaben da kasar za ta yi a karshen makon da ke tafe.
A ranar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris.
“Yayin da aka tunkari zabe a Najeriya, wannan wata dama ce ga al’umar kasar da za a saurari ra’ayinsu, ta yadda za su zabawa kasar makoma mai kyau.” Blinken ya ce a wani sakon bidiyo da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.