ABUJA, NIGERIA - Malam Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a fannin yada labarai ya bayyana cewa shugaba Buhari na kan ganawa da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a kasar.
A yayin wani zaman zauren majalisar dattawa da aka yi ranar Laraba 27 ga watan Yuli ne shugaban marasa rinjaye na jam’iyyar PDP Sanata Philip Tanimu Aduda, da ke wakiltar mazabar birnin tarayyar Abuja mai kananan hukumomi 6, ya nemi shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bada dama a tattauna batun tsaro a kasar da kuma batun tsige shugaba Buhari. Sanata Lawan, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya ki amincewa da bukatar shugaban marasa rinjayen.
Al’amarin dai ya fusata akasarin ‘yan majalisar da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyun adawa inda wasunsu suka fice daga zauren majalisar, a cewar Sanata Istifanus Gyang.
A wani bangare kuma, Sanata Ahmed Babba Kaita, mai wakiltar mazabar Katsina ta Arewa, shiyyar da shugaba Muhammadu Buhari ya fito, wanda ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP a baya-bayan nan, ya ce shi ba maganar tsige shugaban kasa ta dame shi ba illa samar da zaman lafiya a kasar.
Sanata Yusuf A. Yusuf na jam'iyyar APC, da ke wakiltar jihar Taraba ta tsakiya ya ce 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, don haka ya kamata jama'a su ba gwamnati cikakken goyon baya.
Shi ma shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Alhaji Nastura Ashir Shariff, cewa ya yi sai an yi da gaske za’a iya kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Batun ficewar sanatocin jam’iyyun adawa dai na zuwa ne a daidai lokacin da al’amuran tsaro ke kara tabarbarewa musamman a manyan biranen kasar ciki har da Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
‘Yan Najeriya a kusan duk sassan kasar na dada shiga damuwa sakamakon yadda ‘yan ta’adda ke kara shiga cikin mutane.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdurra'uf.