Tafkin da ke tsakanin kasashen Kamaru, Chadi, Najeriya da Nijar, da tsibiran da ba su da adadi, suna cikin manyan wuraren da mayakan Boko Haram na Najeriya da kuma reshenta masu tayar da kayar baya, wato (ISWAP) su ka sami mafaka.
Sojojin kasashen hudu sun farfado da rundunar hadin gwiwa ta (MJTF) a shekarar 2015 domin yakar masu tsattsauran ra'ayi a cikin tafkin bayan kafuwarta a shekarar 1994.
Sojojin sun kaddamar da wani sabon farmaki a cikin watan Maris da nufin "murkushe Boko Haram gaba daya da sauran kungiyoyin ta'addanci da ke addabar tafkin", wani babban jami'in MJTF, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar AFP Lahadi.
Tsakanin Laraba da Juma'a, "akalla 'yan ta'adda 20 ne aka kashe ", in ji kungiyar kawancen.
Babban jami’in na MJTF ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda na da niyar kashe mutane, ya kara da cewa an kai harin ne a Kamaru da kuma Najeriya.
Gamayyar dai ba ta bayar da adadin mayakan jihadin da aka kashe ba tun bayan fara kai farmakin a watan Maris.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a ranar 25 ga Afrilu, ta ce sojojin Nijar sun kashe 'yan ta'adda 30 a yankin Kaji Jiwa da ke jamhuriyar Nijar ta bakin ruwa. Ba a bayyana yaushe ba. MJTF ta kara da cewa soja daya ya mutu.
Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekara ta 2009 kafin ta yadu zuwa kasashe makwabta.
Sama da mutane 36,000 ne aka kashe tun daga lokacin, musamman a Najeriya, kuma an tilastawa miliyan uku barin gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
~ AFP