A ranar Talatar wannan makon ce dai 'yan-bindigan su ka tare ayarin motochin da ke kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda su ka kashe mutane biyu da jikkata mutane goma, sannan a ranar Laraba ma su ka kara datse ayarin inda su sa ce mutane da dama, sai kuma gashi sun kara tare hanyar a jiya Alhamis har ma sun kashe mutane su ka kuma sace mutane da dama.
Alh. Zubairu Abdurra'uf Idris shine Dan-masanin Birnin Gwari, ya kuma bayyana cewa al'umar yankin su na cikin wani hali.
Mai magana da yawun rundunar'yan-sandan jahar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya tabbar, ya ce
datse ayarin motochin da 'yan-bindigan su ka yi cikin kwanaki uku a jere dai, a Laraba ne kawai suka sha da kyar saboda misayar wuta da su ka yi da jami'an 'yan-sanda.
Maganar matsalar hare-haren 'yan-bindiga a wasu sassan jahar Kaduna dai sun yi kamari cikin wannan wata da mu ke ciki har ta kai ga gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya gana da shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin neman mafita.
Yanzu dai hanyoyin fita ko shiga jahar Kaduna sun zama abun tsoro saboda hare-haren 'yan-bindiga domin kuwa ko bayan hanyoyin Kaduna-zuwa-Abuja da kuma Kaduna-zuwa-Birnin Gwarin da ake fargaba, ita ma hanyar Kaduna-zuwa-Zariya yanzu ba ta da tabbas saboda yadda 'yan-bindigan su ka fara tare ta.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: