Rahotanni daga Najeriya na cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da Manjo Christopher Datong, sojan da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da shi a harin da suka kai makarantar horar da sojoji ta NDA da ke Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Wata sanarwa da mataimakin Darektan yada labarai a rundunar sojin Najeriya ta 1, Kanar Ezindu Idamah ne ta bayyana cewa an kubutar da babban jami’in sojan a ranar Juma’a.
Wata gamayyar dakarun Najeriya ce ta ceto Datong a wani samame da aka kai, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan fashin dajin da dama, Idamah ya ce.
Sanarwar ta kara da cewa an kuma lalata sasanonin ‘yan bindigar da dama a yankunan Afaka-Birnin Gwari da ke jihar ta Kaduna.
“Za mu ci gaba da kai samamenmu, har sai mun kama ko mun kashe maharan da suka kashe manyan jami’anmu biyu a harin na NDA.” Idmah ya ce.
A ranar 24 ga watan Agusta ‘yan fashin daji suka kutsa kai cikin kwalejin ta NDA suka kashe sojoji biyu tare da yin garkuwa da Datong.
Rundunar sojojin ta Najeriya ta ce an kubutar da Datong cikin koshin lafiya “amma ya dan samu rauni kuma an yi masa magani an mika shi ga kwalejin ta NDA.”