Kwanannan nan ne jihar Borno da ke Najeriya ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda, wanda ya zo a daidai lokacin da mayakan Boko Haram da dama suke mika wuya ga hukumomi. CP Audu Umar ya sha alwashin kakkabe ragowar mayakan na Boko Haram, tare da yin aiki da sauran hukumomin tsaro a jihar. Hussaina Muhammed ta hada mana wannan.