A Malawi, mutane masu nakasa, dake sana’ar kayan kawa sun dade suna gwagwarmaya da batun wariya da ake nuna musu. Don shawo kan wannan matsalar, wani kamfanin kayan kawa a Malawi, House of Xandria ya shirya bikin baje koli na farko a kasar na mutane masu nakasa. Ga fassarar rahoton Lameck Masina daga Blantyre.