Shahararren kamfanin kera motocin kasar Germany “BMW” na kara kaimi wajen fito da motoci masu amfani da hasken rana, nan da zuwa shekarar 2020. Wanda yake kokarin fito da sababbin kere-kere masu launuka daban daban, zai fitar da sababbin launuka goma sha biyu 12.
Kamfanin ya sanar da hakan ne a jiya, wannan wani yunkuri ne na ganin ya shiga gaban kamfanin da ya fara kirkirar mota mai amfani da caji ta kasar Amurka ‘Tesla’
Mutane da yawa suna tsoron siyen mota mai amfani da caji, sabo da tsada da kuma zamansu motoci dake da wuyar gyara. Amma tun bayan fito da sabuwar motar da kamfanin Tesla, yayi na tsarin ‘Model S’ a shekarar 2012, sai mutane suka fara sakin jiki da sabon tsarin.
Tun daga nan kamfanoni mai kera motoci, ke shiga cikin gasar samar da motoci da basa amfani da mai, wanda hakan yake da matukar muhimanci ga lafiyar mutane, wajen rage yawaitar gurbatar yanayi.
A shekarar 2013 ne dai kamfanin na BMW ya kaddamar da sabuwar motar i3 mai amfani da wuta, kamfanin yace yanzu a shirye yake ya wadatar da motar a ko’ina a fadin duniya. Daga nan zuwa shekarar 2020, motoci masu amfani da wuta zasu kara yawa.
A shekarar 2025 kuwa, kamfanin zai fitar da kirar sababbin motoci 12 da babu wada zata dinga amfani da man fetur, a cewar shugaban kamfanin Mr. Harald Krueger, a watan zantawa da yayi da manema labarai.
Facebook Forum