Hukumar kula da kwallon Kafa ta kasar Ingila (FA) ta na tuhumar mai horas da kungiyar kwallon Kafa na Arsenal, Arsene Wenger bisa kalaman da yayi wa alkalan wasan da suka hura wasansu da kungiyar Westbromwich, ranar lahadi a gasar Firimiya lig ta Ingila mako na 22 inda aka tashi 1-1
Wenger ya nuna rashin jin dadinsa akan bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty) da aka ba Westbromwich, a kusan karshen lokaci wanda hakan yayi sanadiyar Arsene Wenger, yayi kalaman da basu dace ba a cewar hukumar.
Don haka hukumar FA ta ce tana bukatar Wenger, ya kare kansa akan wannan batu da yayi kafinnan da ranar Jumma'a.
Idaa ba'a mantaba a watan janairun shekarar da ta wuce an haramta wa Wenger tsayuwa a layi na wasanni 4 sakamakon cin zarafin mataimakin alkalin wasa na 4 a wasan da Arsenal ta yi da Burnley.
Facebook Forum