Na’urar hangen nesa mai farautar duniyoyi a sararrin samaniya, ta gano wasu karin duniyoyi guda goma, wadanda ba a san da su ba, wanda kuma girma da yanayin su yayi dai-dai da inda dan Adam zai iya rayuwa.
Bayan an kwashe shekaru hudu ana bincike, naurar hangen nesa ta Kepler ta gano duniyoyi arba’in da tara a shiyyar Goldilocks, kuma ta haska bangare daya ne kawai, na shiyyar da take kunshe da kimanin taurari billiyan dari biyu.
Bakwai daga cikin duniyoyin da aka gano, suna da siffar kwallo ne, tamkar duniyar da muke ciki, kuma yanayin su ma sunyi kama da namu duniyar, ba kamar sauran duniyoyi ba da ke bukatar wata duniyar ta kasance kusa dasu, domin dai-daitar yanayin su.
Wannan ba wai yana nufin akwai rayuwa a duniyar bane, amma suna dauke da abubuwan da za a iya rayuwa a cikin su. Masu binciken kimiyya da fasaha, sun ce wannan sakamakon ya basu kwarin gwiwar cewa za a iya samun rayuwa a wani waje.
Shiyyoyi goma na duniyar Goldilock suna cikin duniyoyi dari biyu da sha tara, da hukumar NASA ta bayyana a ranar Litinin din data gabata a cikin shiyoyin da na’urar hangen nesan ta gano, tun lokacin da aka kafa na'urar a shekarar 2009.
An kafa na'urar ne da zummar gano duniyoyin da su kayi kama da duniyar da muke ciki, da kuma wadanda za a iya rayuwa a cikin su. Aikin na’urar ya zo karshe ne a shekarar 2013, sanadiyyar lalacewar tayoyin ta da suke taimaka mata a sararin samaniya.
Facebook Forum