Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Ireland Tayi Watsi Da Umurnin Kungiyar Kasashen Turai Akan Apple


Har ya zuwa yanzu kasashen turai na cigaba da bazoma kamfanin Apple wuta, ministan kudin kasar Ireland, ya bayyana cewar ba zasu turke kamfanin ba, da zummar biyan karin kudaden haraji da aka ce kamfanin sai ya biya ba.

Kungiyar kasashen turai ‘European Commission’ sun nemi kamfanin da ya biya kasar Ireland kimanin dalar Amurka $13B, ministan ya kara da cewar wannan ba abu ne da ya shafi kungiyar ba, wani abu ne na cikin gidajen kasashen.

Ministan Mr. Paschal Donohoe ya kara da cewar ai tsarin harajin kasashen da kamfanin na Apple, yayi amfani da shi, tsari ne da ake da shi, kuma kamfanin ba suyi wani abu da ya sabama dokokin kasashen yankin ba.

Ya kara da cewar, mu ba masu karban harajin wasu kasashe bane, wata jarida ta ruwaito ministan na cewa, kamfanin na Apple sun biya kudin haraji kasa da abun da ya kamata ace sun biya. Amma sai gashi yana kare kamfanin a wannan karon.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG