Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukata Ta Wakoki Na Su Sami Karbuwa Kamar Na Marigayi Shata Da Dan Maraya - Inji Dabo the prof


Umar Ayuba Isah, Dabo the prof
Umar Ayuba Isah, Dabo the prof

Babban fata na bai wuce wakokina su sami karbuwa kamar na su Marigayi Mamman Shata, Dan kwairo da marigayi Dan maraya Jos, kuma ina matukar son cimma wannan buri ne tun ina raye kafin na mutu, zan so inji a kowadanne lunguna da sakuna ana ambaton wakoki na, inji Umar Ayuba Isah ‘mawaki wanda aka fi sani da Dabo the prof Mr. lada goma.

Dabo the prof, ya ce yana amfani da kalmomin da ba kasafai ake amfani dasu ba a zance domin nuna azancin zance da kuma koyar da harshen Hausa.

Matashin ya kara da cewa yana samun azanci ko basirar waka ne ta hanyar sauraron wasu wakokin kasashen waje, ko kalamansu sa’annan ya mayar da su cikin harshen Hausa.

Prof ya ce yana kiyayewa da satar fasaha inda ba ya kuskuren daukar kalma da kalma daga wurin wani mawaki.

Ya ce kalubalen da suke fuskanta bai wuce yadda mawaka basa amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen bunkasawa tare da tallata wakokinsu ba, baya ga matsalar rashin kudi mussamam ma wajen zuba jari a harkar waka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:59 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG