Shahararren kamfanin sada zumuntar nan a yanar gizo, musamman a fagen aika sakon gaggawa, “WhatsApp” ta kaddamar da wani sabon tsari da ma’abota hurda dashi zasu kara jin dadin amfanin da manhajar.
Yanzu haka mutane zasu iya amfani da manhajar WhatsApp wajen inganta yanayin rubutun su, kana da dora wani shafi da zai kai mutun wani shafi ta hanyar saka link a turance. Yanzu haka dai mutun na iya sauya salon rubutun shi a manhajar whataspp, zuwa wani salo mai ban sha’awa.
Haka mutun zai iya canza kala ko yanayin bangon manhajar da kuma yadda yakeso, wasu abokan shi su dinga ganin shi a shafin. Sabon tsarin zai bama mutane sama da milliyan dari biyu damar bayyanar da sha’awar su da abunda suke so a wata.
Tsarin yana dauke da wasu gurabe masu kayatarwa, wanda mutun zai iya canza tsarin duba garin shi 'status' ta yadda sai wanda kawai ya aminta, su duba garin shi balle su san yadda yake. Kamar tsarin ‘Status update’ yadda mutane ke saka hotuna ko bidiyo.
Sai mutun yaso kamin wani ya iya ganin abun da mutun ya saka, haka akwai damar yadda mutun zai iya sanin suwa da suwa suka kalli shafin shi, a kuma wane lokaci. Haka mutun zai iya rubuta wani sako a duk irin hoto ko bidiyo da mutun ya saka.
A shekarar da ta gabata ne kamfanin na whatsapp suka bayyanar da sakamakon yawan mutanen da suke ziyartar shafin, fiye da mutane billiyan daya a rana, da kuma aikwa da sakonnin fiye da billiyan hamsin da biyar a yini.
Facebook Forum