Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makirkirin Manhajar 'Android' Zai Kaddamar Da Sabuwar Wayar Hannu


Shahararren makirkirin manhajar ‘Android’ Andy Rubin, ya nuna aniyar shi ta kirkirar sabuwar wayar hannu, wadda zatayi goggayya da wayar Apple da Google. A kadan daga cikin bayan da ya fitar na wayar tashi, zata zo da karfin kyamara mai zagaye 360, wadda zata dinga daukar hoto a zagayen gaba da baya.

Akwai rade-radin cewar, kudin wayar zai iya kaiwa naira 260,000. Sabuwar wayar zata zo da damar da babu wayar dake da, wanda mutun zai iya hada wayar da kyamara ta waje, ko saka wasu kayan zamanin don samun nagartattun hotuna ko bidiyo.

A cewar masana, wannan wayar tana iya zama wayar da tafi kowace waya zama, wayar jin dadi, sabo da irin tsare-tsare da akayi mata. Ana sa ran wayar zata shiga kasuwa a tsakiyar shekarar nan idan Allah ya kaimu.

Kudin wayar na iya zama kusan daya da kudin wayar iPhone 7, wanda take kaiwa kimanin dallar Amurka $649, kwatankwacin naira 245,000. Duk cikin yunkurin Kamfanin na ganin sun inganta wayar, sun dauki matasa 40, aiki wanda suke amfani da basirar su wajen ganin an samu abun da duniya zatayi alfahari da.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG