Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zomon Da Yafi Kowanne Girma A Duniya, Ya Mutu A Cikin Jirgin Sama


Zomo
Zomo

Jaridar USA Today ta rawaito labarin mutuwar katon zomon da ba’asan dalilin mutuwar sa ba a cikin jirgin United Airlines a hanyar sa ta zuwa Chicago daga Birtaniya, wanda ya zama kari kan abubuwa marasa dadi da suka shafi kamfanin jirgin cikin yan kwanakin nan.

An sami Zomon mai suna Simon dan watanni goma mai tsayin kafa uku a mace bayan jirgin kirar Boen 767 ya sauka a filin jiragen sama na Chicago O’Hare international Airport bayan tasowar sa daga Birnin Landan.

Mai kiwon zomayen Annette Edward ta fadawa jaridar cewa Zomon da ada ake saran yafi kowanne zomo girma a duniya bayan babansa Darius wanda ya rike kambun Zomo mafi girma a duniya da tsahon kafa hudu da inci hudu, an dauke shi ne a tafi dashi zuwa gidan mashurin mutumin da ya saye shi. Har izuwa yanzu ba tantance dalilin mutuwar zomon ba.

Edward ta fadawa jaridar “The Sun” “Likitocin dabbobi sun duba Simon awanni uku kafin a dorashi a jirgi kuma sun tabbatar da lafiyar sa kalau zai iya hawa jirgi” Amma wani abu dai ya faru kuma ina son insan hakikanin abinda ya farun, domin na tura Zomaye da dama a fadin duniya irin haka bata taba faruwa ba. Wanda ya sayi Simon Shahararren mutum ne kuma ransa ya baci kwarai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG