‘Yan wasan kwallon kafa mata na Super Falcons wanda suka lashe kofin matan Afirka na shekarar 2016, a kasar kamaru na cikin kunci na rashin biyansu alawus dinsu.
Tun farko dai hukumar NFF, tayi musu alkawarin biyansu kudaden da ‘yan wasan ke bi bashi tun kafin fara wasan a kasar kamaru.
‘Yan wasan dai sunyi zaman Dirshan ne a wani otel dake babban birnin tarayar Abuja, suka ce bazasu fita daga otel dinba sai An biyasu kudadensu da aka yi masu alkawari.
Wannan bashi karo na farko da Kungiyar ta taba fuskantar irin wannan matsalarba a shekarun baya da suka wuce haka ya taba faruwa tsakanin ‘yan wasan da hukamar NFF, inda ‘yan wasan suka ki fita daga masaukinsu a kasar Afirka ta kudu a shekara 2004.
Sai dai Babban sakataren hukumar NFF, Dakta Mohammed Sanusi, ya ziyarci ‘yan wasan a otel din da suke, kuma ya basu hakuri harma ya nuna rashin biyansu dacewa matsalar tattalin arziki da Najeriya take ciki shiya jawo hakan amma suna kokarin magance wannan matsalar nan ba da jumawaba.