Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Uefa Champion League 2016/2017


A jiya aka fafata a gasar cin kofin zakarun turai na shekarar 2016/2017 a matakin wasan rukuni zagaye na 6 inda kungiyoyi takwas suka samu nasarar shiga zagaye na 16.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta samu nasara akan Borussia Monchenglabach daci 4 -1

Bayern Munich ta doke Atletico Madrid da kwallo 1-0

PSG nada 2 Ludogareth nada 2

Dinamon kyiv ta lallasa Besiktas da kwallaye 6-0

Benfica nada 1 Napoli nada 2

Manchester City tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta Celtic

PSV 0-0 Rostov

Basel bataji da dadiba a hannun Arsenal daci 4-1

Kungiyoyin da sukayi nasarar tsallakawa zuwa matakin zagaye na 16 (Round of sixteen) sune Kamar haka:

Arukunin A, a kwai Kungiyar Arsenal, da take na daya da maki 14, sai PSG, na biyu da maki 12.

Arukunin B, a kwai Napoli, a mataki na daya da maki 11, sai Benfica, a mataki na biyu da maki 8.

Rukunin C, kuwa kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona tayi na daya da maki 15 sai Manchester City, na biyu da maki 9.

A Rukunin D, Atletico Madrid, ce tayi na daya da maki 15 yayinda ita kuma Bayern Munich, ta kasar Jamus tayi na biyu da maki 12.

A yau kuma za'a buga wasannin Sauran rukunin inda kungirar kwallon kafa ta Real Madrid zata karbi ba kuncin Borussia Dortmund

Lyon zata kara da Sevilla

Porto zasu fafata da Leicester City

Ita kuwa Juventus, zasu kece raini ne da Dinamon Zagreb

Bayern Leverkusesn kuwa zasu gwabza da Monaco

Legia Warsaw da Sporting Lisbon

Club Brugge da Kobenhanv

Sai Tottenham zata marabci CSKA Moscow

Za'a fafata wasannin da misalin karfe tara Saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00


  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG