An dangata shaye shaye matasa akan rashin kyakkyawar tarbiyar iyaye da kuma rashin sa idon akan ‘ya’ya su na sanin irin abokan da suke mu’amula dasu.
Malam Ibrahim Abubakar, daya daga cikin masu mahauwara a zauren matasa na shirin muryar Amurka, na yau da gobe akan shaye shayen matasa ne ya bayyana haka.
Yana mai cewa wasu matasa kan shiga kungiyoyi na abokai wadanda basu sami tarbiya ba wanda haka shike haifar da shiga irin wadannan kungiyoyi, abinda tun suna kyamarsa har ya kasance sun fara sha’awa.
Ita kuma Fatima Musa, cewa tayi bangaren mata masu wannna mummunar dabi’a na shaye shaye, akasarinsu suna yi ne saboda samarinsu na sha, tana mai cewa wasu matan aure masu wannan hali mazajensu ne ke taimakamasu wajan samar masu da wadannan kayan sa mayen.
Malaman kuma sun ja hakalin gwamnati da su sai ido da tsaurara dokokin dake tattaren da hukuncin da hana shaye shayen a tsakanin matasa kasancewar matasa sune kashin baya kowace al’uma.dokokin.