Hukumar dake kula da kwallon kafa ta kasar ingila (FA) ta dakatar Sergio Aguero, na Manchester City, wasanni har guda hudu tare da Fernandinho, shi kuma wasa uku na Firimiya lig.
Hukumar tace ta dakatar da Aguero ne bisa mumunar ketar da yayi wa dan wasan baya na kungiyar Chelsea, David Luiz, a wasan da sukayi ranar Asabar da ta gabata a wasan firimiya mako na goma sha hudu 2016/2017 inda aka sha Manchester city, uku da daya wanda nan take aka bashi jan kati (Straight Red Card).
Sakamakon wananan keta ya janyo hatsaniya tsakanin ‘yan wasan Kungiyoyin biyu inda takai ga Fernandinho, ya bankade dan wasan Chelsea, Cesc Fabiegas, har kasa sanadiyar haka shima aka bashi jan Kati.
Bayan haka hukumar ta FA tana tuhumar duka Kungiyoyin biyu Manchester city da Chelsea bisa rashin shawu kan yanwasansu a lokacin hatsaniyar.
Don haka hukumar ta basu wa'adin nan da ranar takwas ga watan disamba na shekarar dubu biyu da goma sha shida da su kare kansu ko kuma su fuskanci hukunci daga hukumar, a cikin wasanin da Aguero da Fernandinho bazasu buga ba sune wasan da za suyi da Leicester City, Watford, Arsenal da kuma Hull City.