Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Firimiya Lig 2016/2017 Mako Na Sha Hudu


A ranar Asabar 3/12/2016, Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 3-1

Sunderland ta doke Leicester City da kwallo 2 da 1

Tottenham ta lallasa Swansea da kwallaye 5 da 0

Crystal Palace ta doke Southampton da ci 3-0

Stoke city ta samu nasara a kan Burnley da kwallo 2-0

Westbromwich nada 3 Wartfotd nada 1

Westham ta sha kashi a hannun Arsenal da ci 5-1

A yau kuma MiddleBrough zasu karbi bakuncin hull City

Da misalin karfe Tara na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da Chadi

A saman teburin na firimiya lig kuwa Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ke rike da saman teburin da maki 34

Arsenal na mataki na biyu da maki 31

Ita kuwa Liverpool na mataki na uku ne da maki 30, yayinda Sunderland take mataki na sha takwas a Kasan tebur da maki 11

Hull City na mataki na sha Tara da maki 11.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:27 0:00

Swansea na mataki na ashirin da maki 9.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG