Shaye shaye da mata keyi na ciwa mutane tuwo a kwarya a jihar Adadez, dake jamhuriyar Nijar, biyo bayan kwararar bakin haure da kuma zaman rashin tabas, a kasashen dake makwabtaka da Agadez, kamar irin su Libiya, da kudanshin kasar Algeria.
Shi dai wannan lamarin na shaye shayen ‘ya’ya mata matasa a jihar Agadez, ya sabawa alada da addinin al’umar yankin arewacin jamhuriyar Nijar.
Hana ‘ya’ya mata auren wadanda suke so ko kuma sasu aiyukan da suka fi karfinsu ko kuma gallaza masu ya Allah daga iyaye ko kuma masu rikonsu yana jefa ‘ya’ta mata shiga cikin irin wannan hali na shaye shaye ko kuma shashenci.
Wata matashiyar Fatima Musa, ta ce anyi mata auren dole ne daga bisani sai ta gudu ta bar garin anan ta ga abokan da take tare dasu suna shaye shaye sai taga cewa ya burgeta daga nan sai itama ta fara.
A cewar malama Salamatu, mai kula da shashen inganta rayuwar ‘ya’ya mata ta ce tsanantawa ‘ya’ya mata da auren dole na cikin abubuwan dake sa ‘ya’ya mata shiga cikin wannan halin na shaye shaye.