Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Kan Mata Ya Waye Suna Karbar Rigakafi - Inji Hassana Salisu Abubakar


Yau mun sami bakuncin wata abokiyar aiki ce mai suna Hassana Salisu Abubakar, wadda ta goge wajan aikin jarida musamman bangaren rahotannin da suka shafi harkokin lafiya, kuma mun tattauna da ita dangane da yadda mata masu juna biyu da kananan ke karbar digon riga-kafi.

Ta ce a yanzu kan mata ya waye sosai domin suna bada hadin kai wajen karbar rigakafi ga mata masu juna biyu tare da kiyayewa wajen amfani da gidan sauro da ma zuwa awo da zarar watannin cikin haihuwa.

Ta ce bulluwar ciwon shan inna da aka samu a ‘yan kwanakin da suka gabata na da nasaraba da sakacin gwamnati mussamam ma a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Babbar shawara ga gwamnati a cewarta it ace, wadanda alhakin abin ya rataya a wuyansu su tabbatar ana shiga lunguna da sakuna domin magance matsalolin karbar riga-kafi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG